Isa ga babban shafi
Isra'ila- Amurka

Kasashen duniya sun mayar da martani kan Tuddan Golan

Majalisar Dinkin Duniya da kasashen Larabawa sun yi watsi da matakin Amurka na amincewa da Tuddan Golan a matsayin yankin Isra’ila, in da Saudiya ke gargadin cewa, matakin zai cutar da shirin zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Shugaba Donald Trump ya sanya hannu kan kudirin amincewa da Tuddan Golan a matsayin yankin Isra'ila.
Shugaba Donald Trump ya sanya hannu kan kudirin amincewa da Tuddan Golan a matsayin yankin Isra'ila. © AFP
Talla

Kasashen Saudiya da Bahrain da Qatar da Kuwait da dukkaninsu ke kawance da Amurka sun soki kudirin shugaba Donald Trump na amincewa da Tuddan Golan a matsayin yankin Isra’ila, in da suka ce yankin na Larabawa ne.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, matakin Trump ba zai sauya matsayin yankin ba kamar yadda yake a doka domin kuwa a cewarta, za ta yi tsayin-daka kan kudurin da Kwamitin Sulhu ya dauka dangane da yankin.

Ita ma Kungiyar Kasashen Turai da ta fitar da sanarwarta gabanin ganawar Trump da Benjamin Netanyahu ta ce, ba za ta goyi bayan matakin na shugaban Amurkan ba.

Turkiya da Lebanon da Rasha har ma da Syria duk sun mayar da martani kan matakin na Trump, in da gwamnatin Syria ke cewa, matakin tamkar kaddamar da hari ne akan ‘yancinta.

Kasashen na duniya sun ce, matakin na a matsayin karan-tsaye ga dokokin kasa da kasa.

A ranar Litinin ne shugaba Trump da ya karbi bakwancin Netanyahu a birnin Washington, ya sanya hannu kan kudurin da ke ayyana yankin Tuddan Golan na Syria a matsayin mallakin Isra’ila.

A shekarar 1967 ne, Isra’ila ta kwace yankin daga hannun Syria a lokacin yakin Gabas ta Tsakiya, yayinda ta hade shi da kasarta a shekarar 1981 duk da cewa kasashen duniya ba su amince da haka ba.

Shugaba Donald Trump ya ce daukar matakin, alama ce da ke tabbatar da cewa gwamnatinsa na goyon bayan Isra’ila sannan kuma za ta bai wa kasar duk wata kariyar da take bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.