Isa ga babban shafi
Amurka-Duniyar wata

Amurka ta cika shekaru 50 da tura mutanenta 3 duniyar wata

Dubun dubatar Amurkawa na bikin cika shekaru 50 cif da nasarar kasar ta aikewa da mutanenta 3 duniyar wata a rana mai kamar ta yau cikin shekarar 1969, wadanda suka samu sukunin isa kan duniyar watan a cikin Kumbon da aka yi wa lakabi da Apollo 11, daga cibiyar hukumar NASA da ke birnin Florida.

Amurkawa 3 da suka isa duniyar wata a tarihi wato Neil Armstrong da Michael Collins da kuma Buzz Aldrin
Amurkawa 3 da suka isa duniyar wata a tarihi wato Neil Armstrong da Michael Collins da kuma Buzz Aldrin NASA / dominio público
Talla

Yau talata Buzz Aldrin mai shekaru 89 da Micheal Collins mai shekaru 88 suka sake haduwa a dai dai wurin da suka tashi zuwa duniyar wata shekaru 50 da suka gabata, tare da kwamandansu Neil Armstrong da ya mutu a shekarar 2012, wanda shi ne na farko daya soma taka duniyar watan.

Kumbon da suke ciki mai suna Apollo 11 ya shafe kwanaki hudu yana tafiya kafin isa kan duniyar wata a ranar 20 ga watan Yuli na shekarar 1969.

Tun bayan kammala aikin mutanen uku da kuma dawowarsu zuwa duniya a shekarar 1972, har yanzu babu kasar da ta sake samun nasarar aikewa da jami’anta zuwa duniyar watan.

A shekarun 1989 da kuma 2004 shugabannin Amurka George H.W Bush da dansa George W Bush suka yi alkawarin sake aikewa da tawagar bincike zuwa duniyar ta wata har ma da duniyar Mars, amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba, saboda rashin samun goyon bayan majalisun dokokin kasar a lokutan da su ke mulki.

Za dai a shafe tsawon mako guda ana gudanar da bikin tunawa da ranar a Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.