Isa ga babban shafi
Amurka

Democrat ta kaddamar da shirin tsige Trump

Jam’iyyar Democrat ta kaddamar da bincike a hukumance kan zarge-zargen da ake yi wa shugaban Amurka Donald Trump na neman taimakon gwamnatin Ukraine domin bata sunan abokin hamayyarsa a siyasance.

Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Daya daga cikin jiga-jigan Democrat kuma shugabar Majalisar Wakilai, Nancy Pelosi ta ce, dole ne shugaba Trump ya fuskanci hukunci saboda ya karya doka, yayin da ta bayyana aikinsa a matsayin karen-tsaye ga kundin tsarin mulki.

Tuni shugaban ya musanta zarge-zargen wadanda ya bayyana a matsayin bita da kullin siyasa.

Sai dai a yayin da Democrat ke tsayin daka wajen ganin an tsige Trump daga kujerarsa, akwai yiwuwar binciken ya gamu da cikas daga bangaren Majalisar Dattawan kasar wadda ke karkashin jagorancin jam’iyyar Republican mai mulkin kasar.

Wannan dambarwa na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun ce, shugaba Trump ya gana da takwaransa na Ukraine, Volodymyr Zelensky, inda ya nemi taimakonsa domin bata sunan Joe Biden, tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka.

Kodayake kawo yanzu, babu cikakken bayani kan abinda Trump ya tattauna da Zelensky, amma Democrat ta zargi shugaban da yi wa Ukraine barazanar dakatar da ba ta tallafin soji da zummar tirsasa mata gudanar da bincike kan zargin Biden da dansa, Hunter da hannu a wata badakalar cin hanci da rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.