Isa ga babban shafi
Faransa-Isra'ila

Masu kyamar Yahudawa ne ke inkarin halascin Isra'ila- Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na ziyara a kasar Isra’ila don halartar taron cika shekaru 75 da ‘yantar da sansanin ihunka banza da ‘yan Nazi suka kafa a garin Auschwitz lokacin yakin duniya na biyu.

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron da takwaransa na Isra'ila Reuvin Rivlin.
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron da takwaransa na Isra'ila Reuvin Rivlin. Reuters
Talla

A ranar farko ta ziyarar, Emmanuel Macron ya gana da Firaminista Benyamin Netanyahu da shugaban Isra’ila Reuven Rivlin, sannan kuma ya shirya kai ziyara a Ramallah don ganawa da shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas kan batun farfado da shirin zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu.

A taron manema labarai na hadin guiwa da takwaransa na Isra’ila Reuven Rivlin, shugaba Macron ya ce duk wanda ke inkarin wanzuwar Isra’ila a matsayin kasa, na daga cikin masu nuna kyama ga Yahudawa.

Shugabannin kasashen duniya fiye da 40 da suka hada da Emmanuel Macron, Vladimir Putin da mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ne za su halarci bikin da za a gudanar gobe alhamis a cibiyar da aka gina a Yaf Vashen don tunawa da Yahudawan da suka mutu a lokacin yakin duniya na biyu.

To sai dai Firaministan Poland ya ce ba zai halarci taron ba, a cewarsa sansanin ihunka banza na Auschwitz a kasar Poland ne, saboda haka a Poland ya kamata a yi wannan taro amma ba a Isra’ila ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.