Likitan China da ya bayyana cutar coronavirus ya mutu
Wani likita dan kasar China da aka muzgunawa bayan ya fito fili ya shaida bayyana cutar masahako ta Corornavirus ya mutu a yau Juma’a, lamarin da ya tayar da hankali tare da harzuka al’umma kan cutar da ta kashe sama da mutane 630 kuma ta ke ci gaba da yaduwa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Akalla mutane dubu 31 sun harbu da wannan cuta da likitan ido Li Wenliang da abokansa suka gano a watan Disamban shekarar da ta gabata.
Cutar ta yadu a China har ma ta tilasta wa gwamnati rufe wasu birane na milyoyin mutane, yayin da aka shiga fargaba a Duniya ganin yadda cutar ta kama mutane sama da 240 a fiye da kasashe 20 a fadin Duniya.
Amurka ta bayyana fatan taimakawa China a fanin bincike,tayin da China ta yi watsi da shi a kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu