Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falasdinawa

Kasashen duniya sun yi wa Isra'ila kashedi kan Falasdinu

Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Larabawa sun yi kiran hadin-guiwa ga Isra’ila da ta yi watsi da shirinta na mamaye wasu yankunan Falasdinawa da ke Yamma ga Kogin Jordan, yayin da mambobin Majalisun Dokokin Turai sama da dubu 1 suka rattaba hannu kan wata wasika da ke adawa da shirin na mamayar.

Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu Adina Valman/Knesset Spokesperson's Office via Reuters
Talla

Majalisar Dinkin Duniyar da Kungiyar Kasashen Larabarawan sun yi wannan kiran ne a yayin wani taro ta kafar bidiyo da ya samu halartar dimbin Ministocin kasashen duniya.

Wannan dai, shi ne taro na karshe da kasashen duniya suka gudanar kafin Isra’ila ta yi gaban kanta wajen aiwatar da shirin mamayar a farkon watan gobe.

A yayin gabatar da jawabinsa, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce, “ Ina kira ga gwamnatin Isra’ila da ta yi watsi da shirin mamayar".

Guterres ya jaddada dadadden muradin kafa kasashe biyu masu cikakken ‘yanci a matsayin hanyar magance rikicin Isra’ila da Falasdinu, inda Birnin Kudus zai kasance babban birnin bangarorin biyu.

Shi kuwa Shugaban Kungiyar Kasashen Larabawa Ahmed Aboul Gheit cewa ya yi, mamayar Isra’ila za ta lalata duk wani yunkurin samar da zama lafiya nan gaba a yankin.

Mambobi sama da dubu 1na Majalisun Dokokin Kasashe Turai daban daban sun rattaba hannu kan  wasikar da ke matukar adawa sa shirin Isra'ila na mamaye yankunan Falasdinawan.

Sama da 'yan Majalisu 200 ne daga Birtaniya kadai suka sanya hannu kan wasikar, yayin da Ofishin  Jakadancin Isra'ila da ke birnin London ya ki cewa uffam kan al'amarin.

An wallafa wasikar ce a jaridu a daidai lokacin da ya rage mako guda Isra'ila ta fara aiwatar da shirin mamayar.

Wannan na zuwa ne a yayin da gwamnatin shugaba Donald Trump ta jaddada goyon- bayanta ga duk wani shiri na mamayar Isra'ila a yankin Yamma ga Kogin Jordan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.