Isa ga babban shafi

Kuskure ne zartas da hukuncin kisa kan masu Fyade- Bachelet

Shugaban Hukumar kare hakkin Dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet ta ce duk da ya ke laifin fyade ga mace na da matukar girma amma kuma yanke masa hukuncin kisa bai dace da shi ba.

Shugabar hukumar kare hakkin dan adam ta Duniya Michelle Bachelet.
Shugabar hukumar kare hakkin dan adam ta Duniya Michelle Bachelet. CRISTIAN HERNANDEZ / AFP
Talla

Yayin da ta ke tsokaci kan yanke hukuncin kan wasu mutane 5 da aka yankewa wadanda suka yi wa wata yarinya mai shekaru 15 fyade a kasar Bangladesh, Bachelet ta ce duk da ya ke yana da kyau a dauki hukunci mai tsauri kan masu aikata irin wannan laifi, hakan bai kuma dace ya zama hanyar cin zarafin wasu ba.

Wannan hukunci shi ne irin sa na farko tun bayan da gwamnatin Firaminista Sheikh Hasina ta yi dokar a cikin wannan mako saboda karuwar aikata laifin.

Bangladesh ta yi dokar hukuncin kisa kan mutanen da suka yi taron dangi wajen fyade, amma dokar ta sanya hukuncin daurin rai da rai kan mutum guda idan ya aikata laifin.

Bachelet ta ce ta fahimci cewar anyi wannan dokar ce domin hana mutane aikata laifin, amma kuma babu wata shaidar da ke tabbatar da cewar hukuncin zai hana mutane aikata laifin.

Shugabar ta ce babu wata shaidar da ke nuna cewar mutanen da ke fuskantar fyade a kasashe da dama na samun kotunan da ke bi musu kadin cin zarafin da aka musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.