UNICEF za ta tallafawa yara miliyan 39 da yaki ya daidaita a gabas ta tsakiya
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya kaddamar da gidauniyar neman dala miliyan 2 da rabi don tallafawa yara miliyan 39 a gabas ta tsakiya, wadanda radadin yake-yake, talauci da annobar coronavirus ya shafa.
Wallafawa ranar:
Babban Daraktan UNICEF a yankin gabas ta tsakiya Ted Chaiban, ya ce yankin na kunshe da yara kanana da ke cikin yanayi na matukar bukata, wanda ya ce sun hada da tasirin radadin yake-yake, talauci da koma-bayan tattalin arziki.
Ya ce asusun ya mika bukatar baya-bayan nan ne don tallafawa yaran da ke cikin matsanancin bukatar jinkai, kuma ke ci gab da samun matsaloli sakamakon bullar annobar COVID 19.
A wata sanarwar asusun na UNICEF ya ce yara na cikin matsanci bukata a yankunan da yaki ya daidaita a Yemen da Syria da Sudan, inda a Yemen yara miliyan 12, ko kuma ma kowane yaro yake neman agaji biyo bayan yakin da aka shafe shekaru 5 ana yi.
A Syria, kusan yara miliyan 5 ne ke bukatar a agaza musu bayan yakin basas aya lakume rayuka sama da dubu dari 3 da 80, ya kuma jefa kasar a cikin matsain tattalin arziki.
A Sudan, yara miliyan 5 da dubu dari 3 na bukatar kama musu, bayan da ambaliyar ruwa da ba taba ganin irinta ba, da kuma matsalar tattalin arziki suka addabi kasar.
A Lebanon kuwa, yara miliyan 1 da dubu dari 9 ne ke dogaro da taimako,biyo bayan fashewar wani abu da ta kashe mutane fiye da 200 ta kuma lalata wasu sassan babban birnin kasar, Beirut a watan Agusta.
Sanarwar ta jaddada cewa ba zai kyautu duniya ta yi gum tana kallon yara cikin matsanancin bukata ba, sakamakon munanan yake yake 2 a tarihi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu