Isa ga babban shafi

Kusan mutane biliyan 2 na fuskantar barazanar harbuwa da Korona - rahoto

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane  biliyan 2 ne ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar korona da wasu cututtuka saboda yadda suke aiki a cibiyoyin kula da lafiya ba tare da samun tsaftataccen ruwa ba.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus. Fabrice Coffrini/Pool via REUTERS
Talla

Rahotan hadin gwuiwa da Hukumar Lafiya da Hukumar UNICEF suka rubuta ya ce aiki a cibiyoyin kula da lafiya ba tare da samun ruwa da tsaftataccen wurin aiki ba kamar tura likitoci, ko masu taimaka musu aiki ne ba tare da basu kayayyakin da zasu karę kań su ba.

Shugaban Hukumar lafiya Tedros Adhanom Gebreyesus ya bayyana samar da ruwa da tsafta a cibiyoyin kula da lafiyar a matsayin ginshikin dakile cutar korona.

Rahoton ya ce ba’a samun ruwa a kowanne cibiyar kula da lafiya guda daga cikin guda 4 da ke duniya, kumą ba’a tsaftace hannu a cibiya guda daga kowanne guda 3, yayın da ba’a samun tsaftataccen bayan gıda a kowanne guda daga cikin guda 10.

Rahotan ya ce wannan matsala tafi kamari ne a kasashe masu tasowa 47 na duniya abinda ke jefa mata masu ciki da jarirai da kuma yara cikin hadari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.