Isa ga babban shafi
Amurka

'Yan Republican na shirin mara baya ga yunkurin tsige Trump kan rikicin Capitol

Wasu Mambobin Majalisar dattawan Amurka sun mara baya ga kudirin majalisar wakilai na tsige shugaban kasar mai barin gado Donald Trump biyo bayan rikicin da ya haddasa sakamakon ingiza magoya bayansa wadanda suka farwa jami’an tsaron Capitol a Larabar da ta gabata.

Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump.
Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump. (AP / JPP)
Talla

Mambobin Jam’iyyar Democrat da ke da karfin iya tsige shugaban a matakin majalisar wakilai, na shirin gudanar da wani taro a yammacin yau don tattauna matakin da za su dauka bayan bukatar Nancy Pelosi na ganin sun kada kuri’ar tsige shugaban.

Dan majalisar dattawan Amurka Sanata Ben Sasse na jam’iyyar Republican ya ce a shirye ya ke ya amince da kudirin majalisar wakilan kan tsige Trump.

Trump wanda ya haddasawa Amurka abin kunya mafi muni bayan tunzura magoya bayansa ta hanyar ikirarin tafka magudi a zaben kasar na watan Nuwamba kawo yanzu bai fito ya bayar da hakuri kan tashin hankali na Capitol daya hallaka mutane 5 ciki har da jami’in tsaro ba.

Matukar dai Majalisar wakilan ta amince da tsige Trump kenan ana bukatar rinjayen kashi 2 bisa 3 na majalisar dattijai wadanda za su kada kuri’a don tabbatuwar tsigewar gabanin rantsar da Joe Biden a ranar 20 ga watan da muke ciki na Janairu.

Tun a jiya Alhamis shugabar Majalisar wakilan Amurkan Nancy Pelosi da shugaban marasa rinjaye na majalisar Dattijai Chuck Schumer suka mika bukatar ganin mataimakin shugaban kasa Mike Pence da ministocin Trump sun yi amfani da tanadin kundin tsarin mulkin kasar na 25 wajen bayar da damar tube shugaban matukar ya gaza sauke nauyin da ke kansa bisa tanadin doka, bukatar da tuni Pence ya yi watsi da ita ta bakin mashawarcinsa.

Yayin rikicin na Shekaran jiya Laraba magoya bayan Trump sun danna kai cikin zauren Capitol tare da tayar da rikici wanda ya tilasta sauyawa ‘yan majalisun waje don basu cikakkiyar kariya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.