Isa ga babban shafi
Rasha

A karon farko murar tsuntsaye ta yadu daga tsuntsu zuwa dan adam

Rasha tace kwararrunta su gano kashin farko na yaduwar cutar murar tsuntsaye ta H5N8 zuwa dan adam, kuma tuni suka sanar da hukumar lafiya ta duniya.

Kajin kasar Turkiya a wani gidan gona dake garin Ziesluebbe, na kasar Jamus.
Kajin kasar Turkiya a wani gidan gona dake garin Ziesluebbe, na kasar Jamus. EPA-EFE
Talla

Kwararrun na Rasha sun bayyana gano kashin farko na yaduwar cutar ga dan adam ne, a tsakanin wasu ma’aikata bakwai dake aiki a wata gonar Kaji dake kudancin kasar, inda aka samu barkewar murar ta H5N8 a watan Disamban da ya gabata.

Bincike dai ya tabbatar da cewar murar ta H5N8 na da mummunar illa tsakanin tsuntsaye, zalika ba a taba samun rahoton yaduwar ta zuwa dan adam ba.

Wani rahoton kwararru ya nuna cewar mutane za su iya kamuwa da nau'ikan murar tsuntsaye na H5N1 da H5N9 da kuma H1N1, ta hanyar tu'ammuli da tsuntsayen kai tsaye, sai dai ba a samun yaduwar murar daga mutum zuwa mutum, kamar yadda binciken hukumar lafiya ta duniya ta tabbatar.

Wani binciken kwararrun kuma ya nuna cewar murar tsuntsaye ta H1N1 na da tasirin kashi 60 cikin 100 na halaka dan adam idan ya kamu da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.