Isa ga babban shafi
Amurka - Tattalin Arziki

Shirin Biden na sake gina Amurka zai lashe dala triliyan 2

Shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar da shirinsa na samar da miliyoyin ayyukan yi da sake inganta ababen more rayuwa a kasar, ciki har da yiwa tsarin sufurinsu gagarumin garambawul, shirin da a dunkule ya ce zai lakume dala triliyan 2.

Shugaban Amurka Joe Biden, yayin gabatar da shirinsa na sake gina Amurka a birnin Pittsburg.
Shugaban Amurka Joe Biden, yayin gabatar da shirinsa na sake gina Amurka a birnin Pittsburg. JIM WATSON AFP
Talla

Yayin jawabin da ya gabatar a daren jiya Laraba Biden ya ce fannin sufuri kadai zai lashe dala biliyan 620.

A karkashin shirin da zai shafe shekaru 8 yana gudana, gwamnatin Amurka za ta inganta titunan da tsawonsu ya kai kilomita dubu 32, gami da gyara dubban gadoji a sassan kasar.

Shugaban Amurke Joe Biden.
Shugaban Amurke Joe Biden. AP - Nati Harnik

Daga cikin hanyoyin da za a samar da kudaden aiwatar da gagarumin shirin na gina Amurka da yi wa tsarin sufurin ta garambawul dai akwai kara yawan harajin da gwamnati ke karba daga kashi 21 zuwa 28.

Sabon kudurin na shugaba Joe Biden na zuwa ne makwanni kalilan bayan da majalisun dokokin kasar suka amince da shirinsa na farfado da tattalin arzikin kasar daga tagayyarar da annobar Korona ta yi masa, wanda ya kunshi kusan dala Tiriliyan 2.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.