Isa ga babban shafi
Amurka - ICC

Biden ya janye takunkuman da Trump ya laftawa kotun ICC

Shugaban Amurka Joe Biden ya janye takunkuman da Donald Trump ya kakkabawa manyan jami’an kotun hukunci kan manyan laifuka ta ICC, ciki har da babbar mai gabatar da karar kotun.

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. AP - Andrew Harnik
Talla

Sai dai yayin sanar da matakin a ranar Juma’a, sakataren harkokin waje Anthony Blinken ya ce har yanzu Amurkan na kan bakanta na adawa da binciken da ICC ke yi na zargin dakarunta da kuma na Isra’ila kan aikata laifukan yaki a Afghanistan da kuma yankin Falasdinu.

A shekarar da ta gabata, tsohon shugaba Trump ta hannun sakataren harokin wajensa Mike Pompeo ya sanar da kakabawa fatou Bensouda takunkuman da suka shafi kudade da haramta mata shiga Amurka, biyo bayan binciken da ta kaddamar kan zarge-zargen da ake yiwa dakarun Amurkan na aikata laifukan yaki a Afghanistan.

A waccacn lokacin dai kotun ta ICC ta kara fusata Amurka ne bayan da ta sake bude bincike kan zargin Isra’ila da aikata laifukan yaki a yankin falasdinawa, abinda ya sanya Amurkan yin tur da kotun tare da yin watsi da hurumin gudanar da bincikarsu da ta ce tana da shi.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.