Isa ga babban shafi
Coronavirus-Rigakafi

Rigakafin Korona ya raba kawunan masu arziki da matalauta

Bisa dukkan alamu batun samar da allurar rigakafin cutar Korona ya raba kawunan manyan kasashen duniya masu arziki da kuma marasa karfi musamman na Afrika.

Kwalaban rigakafin cutar Korona
Kwalaban rigakafin cutar Korona AP - Rafiq Maqbool
Talla

Tun bayan nasarar gwajin rigakafin Korona da aka samar, har yanzu kasashen duniya matalauta na ci gaba da zura ido domin samun cikakken tallafi daga takwarorinsu mawadata.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya gaskata banbancin ratar da kasashen mawadata suka bai wa matalauta, yana mai cewa lamarin babu dadi ko kadan, yayin da ya yi gargadin cewa, muddin aka gaza wadata kananan kasashen, to shakka babu  nasarar da aka samu tamkar ta mai hakar rijiya ne.

A cewar shugaban na WHO, a bana kawai hukumarsa na bukatar kudaden da suka kai Dala biliyan $26 don ganin an cimma nasara a  tsare-tsaren da aka  shimfida na kawar da wannan annoba daga doran-kasa.

Kungiyar Bada Agaji ta Oxfam na ganin cewa, za a dauki shekaru akalla 10 kafin kananan kasashen duniya su gyagije daga barnar da cutar coronavirus ta yi musu.

Duk da tsarin Covax da ke da burin wadata kasashen duniya da rigakafin ba tare da fifita wasu ba da kuma yadda  manyan kamfanonin samar da rigakafin ke ci gaba da kokarin wadata kasashen duniya da su, amma kasashe matalauta na kara dimaucewa saboda yadda ake binciko sabbin na'ukan wannan shu'umar cuta, abin da suke ganin zai kara dagula musu lissafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.