Baƙi basa cikin mutane dubu 60 da zasu halarci hajjin bana - Saudiya
Kasar Saudi tace zata baiwa mazauna kasar kimanin dubu 60 kachal da damar gudanar da aikin hajjin bana saboda dakile yaduwar annobar korona.
Wallafawa ranar:
Cikin sanarwa da hukumomin kasar suka fityar ta nuna cewa mazauna Saudiyan baki da ‘yan kasar da suka karbi allurarn rigakafin korona kadai za’a baiwa damar sauke faralin.
Aikin hajjin, wanda zai gudana a karshen watan Yuli, zai iyakance ga masu kasa da shekaru 65, da basu nuna wani alamun rashin lafiya ba.
Zai kasance shekara ta biyu a jere da ba’asamu sahale aikin hajjin yadda aka saba ba, saboda barkewar annobar coronavirus, inda a bara musulmai dubu 10 kacahal suka samu sauke farali, sabanin sama da miliyan 2.5 da suka gabatar da aikin a shekarar 2019 kafin bullar cutar.
Aikin hajji dai- wajibi ne ga musulmai masu hali a kalla sau daya a rayuwarsu - galibi ya kan tattara miliyoyin mahajjata zuwa birnin na Makka cikin yanayin cunkoso, wanda ya sa ake fargaba zai iya zama silar bazuwar cutar cikin sauri.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu