Isa ga babban shafi
AMURKA-SHARI'A

Kotun koli ta wanke Bill Cosby daga tuhumar cin zarafi

Wata kotu a Amurka ta wanke fitaccen mai wasan ban dariyar talabijin din kasar Bill Cosby da aka daure a gidan yari saboda samun sa da laifin baiwa wata mata kwaya da kuma yin lalata da ita shekaru 15 da suka gabata.

Bill Cosby
Bill Cosby REUTERS/Mark Makela
Talla

Cosby mai shekaru 83 ya fice daga gidan yarin SCI Phoenix dake da nisar kilomita 56 daga arewa maso yammacin Philadelphia da misalin karfe 2.30 agogon Amurka yau laraba kamar yadda wani jami’in kula da gidan yarin ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa.

Sakin na sa ya zo ne bayan hukuncin kotun kolin Pennsylvannia wadda tace ba’a yi masa adalci ba lokacin shari’ar da aka masa a shekarar 2018 lokacin da aka tuhume shi da cin zarafin Andrea Constand a katafaren gidan sa a shekarar 2004.

 Bill Cosby lokacin da kotu ta same shi da laifi
Bill Cosby lokacin da kotu ta same shi da laifi AFP

Alkalin kotun ya bayyana hukuncin sa mai shafuka 79 inda ya soke hukuncin daurin da aka masa ya kuma bukaci sakin Cosby domin komawa gidan sa.

Bill Cosby yayi suna a cikin shirin sa na ban dariya mai suna ‘I Spy’ a shekarun 1960 da kuma ‘The Cosby Show’ wanda yake fitowa a matsayin uba kuma likita a shekarun 1980 kafin shari’ar da ta zubar da kimar sa a idon duniya.

Hukuncin daurin da aka masa shine na farko da ya shafi wani fitaccen mutum tun bayan zargin cin zarafin mata da aka fuskanta a kasashen duniya da aka yiwa lakabi da #MeToo.

Kafin sakin sa yau Cosby ya kwashe sama da shekaru 2 a gidan yari daga hukuncin da aka masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.