Mai dakin marigayi shugaban Haiti ta yi magana a karon farko
Mai dakin shugaban kasar Haiti da aka raunata a harin da ya lakume ran mijinta Jovenel Moise ta yi magana a karon farko a ranar Asabar tun bayan mummunar raunin da ta ji, inda ta yi kira ga al’ummar kasar da kada su karaya.
Wallafawa ranar:
A wani sakon murya da aka wallafa ashafinta na Twitter, Martine Moise ta bayyana godiya ga Allah da ya yi mata tsawon kwana, kwanaki 3 bayan da wasu suka harbe mijinta har lahira a gidansa.
Ministan yada labarai da al’adu na kasar Pradel Henriquez ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran Faransa sahihancin sakon.
Hukumomin Haiti sun ce wata tawagar mahara mai mutane 28 ne suka fasa gidan shugaban kasar suka aika da shi lahira.
Ya zuwa yanzu an kama 17 daga cikinsu, aka kuma kashe akalla 3, yayin da ake ci gaba da farautar sauran.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu