Isa ga babban shafi
Haiti

Haiti ta bukaci taimakon Amurka da MDD bayan kisan shugaban kasar

Kasar Haiti ta nemi taimakon Amurka da Majalisar Dinkin Duniya wajen ganin dakarunsu sun tsare mata wurare masu muhimmaci da suka hada da tashoshin jiragen ruwanta da na sama, bayan kisan gillar da aka yi wa shugaban kasar Jovenel Moise.

Jami'an tsaron Haiti a wajen fadar shugaban kasa bayan kisan gillar shugaban kasa Jovenel Moise
Jami'an tsaron Haiti a wajen fadar shugaban kasa bayan kisan gillar shugaban kasa Jovenel Moise VALERIE BAERISWYL AFP/File
Talla

Tuni Amurka ta ce za ta tura jami’an FBI da wasu zuwa Port-au-Prince, kwanaki biyu bayan kisan shugaba Moise a gidansa.

Da yake tabbatar da bukatar, bayan ganawa da sakataren harkokin wajen Amurka da wakilin Majalisar Dinkin Duniya, Ministan harkokin zaben Haiti Mathias Pierre, yace suna fargabar akwai yiwuwar sojojin haya za su iya lalata wasu muhimman wurara da kaddarorin gwamnati don sake haifar da rudani

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka da Pentagon duk sun tabbatar bukatar da Haiti tayi, na taimakon tsaronta da kuma bincike kan kissan gillar, amma ba su fayyace ko za a tura sojojin Amurka zuwa kasar ba.

Majalisar Dinkin Duniya ba ta ba da amsa nan take kan bukatar da Haiti ba,  amma wata majiyar diflomasiyya ta Majalisar ta nuna akwai bukatar amincewar Kwamitin Tsaro kafin daukar mataki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.