Isa ga babban shafi
Haiti

Kwamitin tsaro na MDD zai yi zama na musamman kan kisan shugaban Haiti

Kwamtin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana kaduwa a game da kisan shugaban kasar Haiti, Jovenal Moise, wanda aka bi shi har gida aka yiwa kisan gilla a Larabar nan.

Shugaban kasar Haiti Jovenel Moïse da wasu mahara suka yiwa kisan gilla har gidansa.
Shugaban kasar Haiti Jovenel Moïse da wasu mahara suka yiwa kisan gilla har gidansa. © Dieu Nalio Chery/AP
Talla

Mambobin kwamitin sun kuma bayyana damuwa kan halin da mai dakin shugaban, Martine Moise ke ciki bayan samun rauni sakamakon harbinta da bindiga da maharan suka yi a jiya.

Shugaban Amurka Joe Biden, wanda ya bayyana rashin jin dadinsa a game da wannan kisan gillar ya ce akwai bukatar karin bayani a game da al’amarin, a bangare guda, Firaministan Birtaniya Boris Johnson yayin bayyana kaduwarsa da kisan, ya yi kira da a kwantar da hankula a kasar ta Haiti, yana mai yi wa al’ummar kasar ta’aziyya.

Tarayyar Turai, ta bakin babbar jakadanta, Josep Borrell  ta  yi kashedin cewa kisan shugaba Jovenel Moise ka iya ta’azzarar tashin  rikici a kasar ta yankin Caribean, tana mai cewa dole ne a kama tare da gurfanar da wadanda suka aikata aika aikar a gaban kuliya.

A  Alhamis din nan kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai gudanar da wani taron gaggawa game da kisan shugaba Jovenal Moise, kamar yadda Amurka da Mexico, wadanda mambobin wucin gadi ne a kwamitin suka bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.