Isa ga babban shafi
Haiti

Mahara sun yiwa shugaban kasar Haiti kisan gilla a gidansa

Firaministan rikon kwarya na Haiti Claude Joseph ya tabbatar da yiwa shugaban kasar Jovenel Moise kisan gilla a gidansa yau laraba, yayin wani farmaki da ya kai ga jikkata matarsa.

Shugaban kasar Haiti Jovenel Moïse wanda tsageru suka yiwa kisan gilla a gidansa.
Shugaban kasar Haiti Jovenel Moïse wanda tsageru suka yiwa kisan gilla a gidansa. © Dieu Nalio Chery/AP
Talla

Kisan gillar ga shugaba Jovenel Moise ya sake tabbatar da hadari baya ga karuwar matsalar tsaron da kasar ta yankin Caribbean ke gani da kuma rikicin siyasar da ya dabaibayeta a bangare guda kuma aikin garkuwa da mutane na ci gaba da tsananta.

A jawabin da ya gabatar lokacin kadan bayan kisan shugaban, Firaministan rikon kwaryar na Haiti Claude Joseph ya ce yanzu shi ne zai ci gaba da jan ragamar kasar, yayinda ya roki al’ummar kasar da su kwantar da hankulansu yana mai cewa jami’an tsaro na daukar matakan da suka dace don tabbatar da tsaron al’umma.

Kalaman na Joseph ya bayyana cewa mutanen da suka yiwa shugaban kisan gilla baki ne da suka shiga kasar, kuma bayanai sun nuna suna magana ne da turancin Ingilishi da kuma Spaniyanci.

Haiti da ke matsayin matalauciyar kasar a kaf takwarorinta na nahiyar Amurka, shugaba Moise ya dauki tsawon lokaci y ana mulki, duk barazana da kuma bukatar ajje mukaminsa.

Baya ga zaben kasar da coronavirus ta tilasta dagewa Haiti kuma na shirin yiwa kundin tsarin mulkinta kwaskwarima nan da watan Satumba.

Tuni dai shugabannin kasashe suka fara aikewa da sakon ta’aziyya ciki har da Firaminista Boris Johnson yayinda Jamhuriyyar Dominica ta sanar da kulle iyakokinta da kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.