An yi yunkurin juyin mulki a Haiti
Ministan shari’ar Haiti Rockefeller Vincent ya ce hukumomin tsaron kasar sun samu nasarar dakile yunkurin wasu gungun mutane na yin juyin mulki.
Wallafawa ranar:
Vincent yace yayin yunkurin juyin mulkin, gungun mutanen sun yi kokari kashe shugaban kasar ta Haiti Jovenel Moise amma hakarsu bata cimma ruwa ba.
Cikin sanarwar da ya fitar ministan shari’ar na Haiti ya kara da cewar daga cikin masu neman kifar da gwamnatin kasar akwai jami’ai masu rike da manyan mukamai.
Lamarin na zuwa ne a yayin da rikicin siyasa ke neman barkewa sakamakon takaddama kan lokacin karewar wa’adin shugabancin Jovenel Moise.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu