Isa ga babban shafi

Fira Ministan kasar Haiti ya yi murabus

Fira Ministan kasar Haiti, Jack Guy Lafontant, yayi Murabus, sakamakon, tashe-tashen hankula a sassan kasar da ke dada kamari, da suka bada damar sace tarin dukiya, bayan da ‘yan kasar suka soma zanga-zangar adawa da shirin gwamnatinsa na kara farashin man fetur.

Daya daga cikin yankunan kasar Haiti da zanga-zangar adawa da gwamnati ta juye zuwa tashin hankali.
Daya daga cikin yankunan kasar Haiti da zanga-zangar adawa da gwamnati ta juye zuwa tashin hankali. HECTOR RETAMAL / AFP
Talla

Fira Minista Lafontant ya mika takardar yin murabus din ce ga zauren majalisar wakilan kasar, da ke shirin kada kuri’ar rashi gamsuwa da gwamnatinsa, wadda ka iya bada damar tsige shi.

A makon da ya gabata ne gwamnatin Haiti da ke fama da durkushewar tattalin arziki, ta sanar da shirinta na kara farashin man fetur da kashi 38, Iskar gas da kashi 47, yayinda kuma ta ke shirin karafa farashin Kalanzir da kashi 51.

Shirin kara farashin albarkatun man fetur din ce ta haddasa gudanar da zanga-zanga a sassan kasar inda mutane 4 suka hallaka, hakan ta sa tilas gwamnatin kasar ta Haiti ta jingine batun kara farashin.

A watan Fabarairun shekarar 2017, tsohon Fira Minista Lafontant ya karbi shugabancin ofishin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.