Isa ga babban shafi
Haiti

Rikicin siyasar Haiti ya dauki sabon salo

Rikicin siyasar kasar Haiti na dada kamari sakamakon nada wani mutum da ‘yan adawa suka yi a matsayin shugaban kasa da zummar korar shugaba Jovenel Moise wanda suka ce wa’adin mulkinsa ya kare.

Shugaban kasar Haiti Jovenel Moise.
Shugaban kasar Haiti Jovenel Moise. REUTERS/Valerie Baeriswyl/File Photo
Talla

A wani faifan bidiyon da aka rabawa manema labarai, alkalin kotun kolin kasar Joseph Mecene Jean Louis mai shekaru 72 yace ya amince da nadin da ‘yan adawar da kungiyoyin fararen hula suka masa na zama shugaban rikon kwarya.

Sabon yunkurin ‘yan adawar dai na zuwa ne bayan da a ranar Lahadi hukumomin tsaron kasar suka dakile yunkurin juyin mulki da kokarin kashe shugaba Moise, inda kawo yanzu aka kame akalla mutane 23 ciki har da fitattun masu rike da manyan mukaman gwamnati.

Sai dai kasar Amurka ta bayyana goyan bayan ta ga shugaba Moise, yayin da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewar yana sanya ido kan abinda ke faruwa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.