Isa ga babban shafi
IRAN-AURE

Iran ta samar da manhajar hada aure ga matasa

Kasar Iran ta kaddamar da wata manhaja da zata dinga taimakawa jama’ar kasar musamman matasa kulla auren da zai dore sabanin hanyoyin da ake amfani da su yanzu haka.

Shugaban Iran Ebrahim Raisi
Shugaban Iran Ebrahim Raisi AP - Ebrahim Noroozi
Talla

Gidan talabijin din gwamnatin kasar Iran ya sanar da sabuwar manhajar wadda aka yiwa suna Hamdam da harshen Farsanci, wadda zata dinga baiwa masu ziyarar ta damar shiga domin lalubo wadanda suke so su aura a saukake.

Kanar Ali Mohammed Rajabi, shugaban Yan Sandan dake kula da yanar gizo yace wannan ce manhaja guda daya tilo da gwamnati ta amince da ita domin kulla aure.

Kanar Rajabi ya bayyana cewar daga wannan lokaci duk sauran manhajojin da ake amfani da su a cikin kasar sun zama haramtattu saboda babu wadda hukuma ta amince da ita.

Cibiyar al’adu ta Tebyan ta samar da manhajar ta Hamdam wadda tace tana amfani da fasahar zamani wajen samarwa mabukata irin abokiyar zaman da suke bukata domin daura aure na din-din-din.

Matan Iran dake amfani da matakan kariya daga cutar korona
Matan Iran dake amfani da matakan kariya daga cutar korona AFP/File

Shugaban Tebyan Komeli Khojasteh ya bayyana cewar tarbiyar da aka saba amfani da ita wajen aure da zaman iyali na tabarbarewa, saboda haka wannan manhajar zata bada damar samar da iyalai masu inganci.

Kanar Rajabi yace rajistar masu amfani da wannan manhajar kyauta ce saboda baiwa jama’a damar cin gajiyar ta.

Hukumomin Iran cikin su harda shugaban addini Ayatollah Ali Khamenei sun bayyana damuwa akan yadda jama’a basa yin aure da wuri a cikin kasar abinda ke haifar karancin yaran da ake haifa kowacce shekara.

Mata a Iran lokacin kada kuri'a
Mata a Iran lokacin kada kuri'a AFP

A watan Maris Majalisar dokokin Iran ta amince da wata doka wadda zata taimakawa jama’ar kasar tare da ma’aurata wajen basu tallafin gina iyalai.

Dokar ta bukaci gwamnati da ta taimakawa masu shirin aure da kuma karfafawa masu yara biyu wajen kara yawan su da kuma dakile masu zubar da ciki.

Yanzu haka wannan doka na jiran amincewar Majalisar koli ta kasar da ake kiras‘Guardin Council‘.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.