Isa ga babban shafi

'Yan Taliban na ci gaba da samun nasara a yakin da suke yi a Afghanistan

Mayakan Kungiyar Taliban sun kama birni na biyu a kasar Afghanistan, wato birnin  Sheberghan, mafi girma a yankin arewacin kasar da ya fada hannun su kasa da sa’o’i 24

Mayaka 'Yan taliban
Mayaka 'Yan taliban AP - Rahmat Gul
Talla

Mayakan kungiyar na amfani da shafukan sadarwa tare da kira ga jama’a a yankin Zaranj da su shirya musu kyakyawar tarbo a ci gaba da kai munanan hare haren da suke yi yanzu haka a sassan Afghanistan.

Rahotanni sun bayyana hango mayakan dauke da tutoci cikin motocin dakarun Afghanistan da suka yi nasarar karbewa daga hannun sojojin kasar.

Wannan yanayi na dada karya gwuiwar dakarun gwamnati, kamar dai yadda wani babban jami’in gwamnatin kasar ya shaidawa kamfanin dillanci  labaran Faransa na AFP, wanda ya kara da cewar yanzu haka da dama daga cikin sojojin gwamnati sun soma ajiye kaki tare da barin rundunnonin su dake fagen daga.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani taro na musamman jiya juma'a domin tattauna rikicin Afghanistan sakamakon hare haren da kungiyar Taliban ta zafafa a cikin kasar da kuma barazanar da yake yiwa daukacin kasar da kuma yankin baki daya.

A sanarwar da ta gabatar, Kungiyar Taliban ta hannun kakakin ta Zabihullah Mujahid ta sha alwashin ci gaba da kai hare hare akan manyan jami'an gwamnatin Afghanistan wadanda suka bada umurnin kai musu hari a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.