Isa ga babban shafi
Afghanistan-Taliban

Afghanistan ta zargi Amurka da haddasa mata rikici

Dakarun Afghanistan sun yi wata fafatawa da mayakan Taliban domin dakile yunkurinsu na kwace babban birnin kasar, bayan hare-haren karshen mako da mayakan suka kai kan manyan biranen kasar, a daidai lokacin da Amurka ke shirin daukar dubban ‘yan gudun hijirar kasar ta Afghanista da ke ci gaba da tserewa.

Fafatawa ta tsananta a Afghanistan tun bayan da Amurka ta fara janye dakarunta
Fafatawa ta tsananta a Afghanistan tun bayan da Amurka ta fara janye dakarunta JAVED TANVEER AFP
Talla

Fada ya kaure a Lashkar Gah babban birnin lardin Helmand, inda 'yan Taliban suka kaddamar da hare-hare a tsakiyar birnin da gidan yari - sa'o'i kadan bayan da gwamnati ta sanar da tura daruruwan kwamandojin soji zuwa yankin.

Mayakan Taliban sun kai hari a cikin manyan larduna uku  da suka hadar da Lashkar Gah da Kandahar da Herat  bayan wani kazamin fada da aka yi a karshen mako wanda ya yi sanadiyyar tserewar dubban fararen hula.

A yayin da jami’an tsaron kasar ke kokarin ganin sun dakile kungiyar Taliban, shugaba Ashraf Ghani ya zargi gwamnatin Amurka da kawo tabarbarewar tsaro a Afghanistan, inda yake ganin matakin janyewar zai haifar da kalubale.

Furucin nasa ya zo ne a daidai lokacin da Amurka ta ce za ta dauki dubban 'yan gudun hijirar Afghanistan yayin da tashin hankali ya mamaye fadin kasar.

Rikici ya tsananta tun farkon watan Mayu, inda masu tayar da kayar bayan ke cin karensu ba babbaka a daidai lokacin da dakarun wanzar da zaman lafiya karkashin jagorancin Amurka bayan suke gab da kammala ficewa daga kasar, bayan kusan shekaru 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.