Isa ga babban shafi
Afghanistan

Kungiyar Tarayar Turai ta ce duniya za ta maida Taliban saniyar ware

Kungiyar Tarayar Turai ta gargadi mayakan kungiyar Taliban da cewa za’a  maida su saniyar ware muddin suka kwace mulkin kasar Afghanistan ta yaki da suke yi.

Tambarin kungiyar Tarayar Turai EU
Tambarin kungiyar Tarayar Turai EU © Photo: AP / Montage: Studio graphique FMM
Talla

Shugaban hulda da kasashen waje na Kungfiyar Tarayar Turai Josep Borrel ya fadi ciki wata sanarwa a Brussels cewa muddin Taliban ta karbe iko a Afghanistan to kuwa kasashen duniya za su ki muamulla da ita.

Yayi bayanin cewa burin kungiyar Tarayar Turai shine su yi hulda mai kyau da karko da kasar Afghanistan, don ganin irin ci gaba da aka samu wajen ‘yancin  mata da matasa da kananan yara mata cikin shekaru 20 da suka gabata bai kamata a sukurkuta ba.

Sanarwar ta bukaci kungiyar Taliban da ta gaggauta tsagaita wuta a yakin da take yi don karbe iko a fadin kasar Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.