Amurka za ta tura Dakaru 3,000 Afghanistan don kwaso mata Amurkawa
Gwamnatin Amurka na Shirin tura Dakarunta dubu uku Afghanistan don tattaro ma ta ‘yan kasar ta zuwa gida sakamakon kazancewar yaki da ake yi tsakanin Dakarun Afghanistan da mayakan Kungiyar Taliban.
Wallafawa ranar:
Ma'aikatar Tsaron Amurka Pentagon ta sanar cewa Dakarun ta za su taimaka ta kwashe ma'aikatan ta dake ofishin jakadanci dake kasar ta Afghanistan.
A cewar Kakakin ma'aikatar Tsaro na Amurka John Kirby Dakarun Bataliya uku za su fara isa filin jiragen sama na tunawa da Hamid Karzai dake Kabul cikin sao'i 24 zuwa sao'i 48.
Yanzu haka rahotanni na cewa Dakarun Gwamnatin Afghanistan sun tsere daga gari na uku wajen girma a kasar wanda yake kusa da birnin Kabul, kuma mayakan kungiyar Taliban sun kwace.
Mayakan kungiyar Taliban yanzu haka suna rike da arewaci da kudanci da yammacin kasar ta Afghanistan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu