Amurka ta kaddamar da allurar covid 19 zagaye na uku ga yan kasar
Amurka ta kaddamar da zagaye na uku na yiwa mutan kasar allurar rigakafin cutar covid da aka sani da sunan Pfizer ko Moderna zagaye na uku.
Wallafawa ranar:
Mutanen da wannan allurar ta shafa sun hada da masu rauni a garkuwar jinkin su,musaman wanda aka yiwa alluran farko da na biyu da kuma ke nuna alama ta rashin lafiya.
Hukumar kasar dake kulla da ingancin maguguna FDA ta tabbatar da cewa ta na da alkaluma dake nuna mata cewa akwai mutanen dake da rauni a garkuwa jinkin su wandada aka yiwa alluran da farko da kuma ya dace a yi musu wata allurar zagaye na uku.
Hukumar ta bayyana cewa wannan mataki bai shafi wandada ke cikin koshin lafiya ba yayinda alkaluma na nuni cewa kusan Amurkawa kashi 2 da dingo 7 cikin dari musaman dattijai ne wannan mataki zai shafa da yawan su ya kai milyan 7.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu