Isa ga babban shafi
Amurka-George W. Bush

Janye dakarun Amurka da NATO daga Afghanistan kuskure ne babba

Kungiyar Taliban ta yi ikirarin cewa dakarunta sun kame mahimmiyar hanyar nan ta Spin Boldak, wacce ta hade iyakar Afghanistan da Pakistan, a yayin da tsohon shugaban Amurka George W. Bush ke caccakar matakin janye dakarun NATO da na Amurka a kasar, yana mai bayyana shi a  matsayin kuskure babba.

George W. Bush tsohon shugaban Amurka.
George W. Bush tsohon shugaban Amurka. Getty Images via AFP - CLIFF HAWKINS
Talla

Ma’aikatar cikin gida ta Afghanistan ta musanta wannan ikirari na kungiyar Taliban, duk da cewa hotunan da ke nuna mayakan kungiyar su na holewa a kan iyakar sun karade shafukan sada zumunta. Zalika, mazauna yankin  sun tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran Faransa da aukuwar al’amarin.

Spin Boldak ne yankin kan iyaka na baya bayan nan da Taliban suka karbe a cikin ‘yan makonnin nan a kokarin  da suke na datse hanyoyin samun kudin shiga na gwamnatin kasar.

A yayin da yake dada bayyana cewa  gwamnati Afghanistan ta rasa iko da jyankuna da dama, tsohon shugaban Amurka  George W. Bush y ace shugaba Biden ya tafka babban kuskure, yana mai cewa an bar fararen hula a hannun wadanda ya kira azzalumai da ke musu kisan mummuke.

Tsohon shugaban na Amurka a karkashin jami’iyyar Republican, wanda shi ne ya aike da dakaru Afghanistan a shekarar 2001, biyo bayan hare haren da aka kai kasar a ranar 11     ga watan Satumba, ya ce ya yi amannar cewa shugabar Jamus Angela Merkel tana tare da shi a wannan ra’ayi nasa.

A farkon watan Maris ne Amurka da NATO suka fara janye dakarunsu daga Afhanistan, kuma ana sa ran za su kammala janyewa a ranar 11 ga watan Satumba, bayan sun shafe shekaru 20 a kasar da yaki ya daidaita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.