Isa ga babban shafi
RIKICIN-AFGHANISTAN

Shugaban Afghanistan Ghani ya gudu daga kasar

Shugaban kasar Afghansitan Ashraf Ghani ya gudu ya bar kasar sa’oi bayan kungiyar Taliban ta bukaci mayakan ta da su jinkirta shiga birnin Kabul sakamakon nasarorin da suke samu akan sojojin gwamnati.

Shugaba Ashraf Ghani
Shugaba Ashraf Ghani © 路透社图片
Talla

Mataimakin shugaban Abdullah Abdullah ya sanar da ficewar Ghani daga cikin kasar a shafin sa na Facebook kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito.

Abdullah yace shugaban ya gudu ya bar jama'a cikin mummunar yanayi, kuma Allah zai kama shi da laifin yin haka lokacin da za'a masa hukunci.

Mataimakin shugaban bai bayyana inda Ghani ya tafi ba, amma kafofin yada labaran kasar sun ce ya tafi Tajikistan ne, inda ake saran ya samu mafaka.

Rahotanni sun ce mayakan Taliban sun yi wa birnin Kabul kawanya inda suke bukatar karbar iko daga hannun gwamnatin Ghani cikin ruwan sanyi, yayin da sojojin kasar suka gaza kare jama’a tun bayan ficewar dakarun Amurka da na kungiyar tsaro ta NATO.

Karbe iko da birnin kabul zai baiwa Taliban damar komawa karagar mulki tun bayan kawar da ita da sojojin Amurka suka yi bayan harin da aka kai mata na ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2001.

Kakakin kungiyar Taliban yace sun baiwa mayakan su umurnin yin dakatawa a wajen birnin domin bada damar tattaunawa domin karbar mulki cikin ruwan sanyi.

Taliban tace har zuwa lokacin da gwamnatin Ghani zata mika musu iko da birnin, mulki da hakkin samar da tsaron Kabul na hannun sojojin gwamnati ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.