Isa ga babban shafi

Yan Taliban sun kama hanyar zuwa babban birnin kasar Kabul

Mayakan Taliban na ci gaba da sa kai zuwa babban birnin kasar Kaboul,mayakan kungiyar Taliban na samun gaggarumar nasara bayan kwace karin garuruwa yayin da Amurka da Birtaniya ke kan hanyar kai dubban sojoji domin kwashe Yan kasashen su da suka makale a birnin Kabul.

Ismail Khan, daya daga cikin Shugabanin kabilu dake yakar yan Taliban da aka kama a Heralt
Ismail Khan, daya daga cikin Shugabanin kabilu dake yakar yan Taliban da aka kama a Heralt via REUTERS - TALIBAN HANDOUT
Talla

Shugaban kasar Ashraf Ghani ya koka dangane da rashin ko karancin kayan yaki musaman jirage da kasashen Duniya suka yi masa alkawali a baya.

Shugaban ya ce kam yanzu bau abinda ya rage banda mayar da hankali ga hanyoyi ko dabaru na murkushe yan Taliban dake ci gaba da sa kai zuwa babban birnin kasar Kabul.Manyan kasashen Duniya na ci gaba da kwashe yan kasar su, a dai-dai lokacin da Faransa ta soke batun baiwa wasu yan kasar dake zaune Afghanistan takardar izinin dawwowa gida.

Mayakan Taliban a Afghanistan.
Mayakan Taliban a Afghanistan. - AFP

Umurnin kwashe Yan kasashen wajen ya biyo bayan kwace iko da Kandahar da Taliban tayi wanda shine birni na biyu mafi girma, yayin da mayakan suka nufi birnin Kabul, babban birni guda da ya rage bai fada hannun su ba.

Gaggauta kwace garuruwa da kungiyar Taliban keyi ya baiwa jama’ar kasar da kungiyar kawancen Amurka wadda ta kashe biliyoyin daloli wajen kifar da gwamnatin Taliban bayan harin 11 ga watan Satumbar da aka kai Amurka kusan shekaru 20 da suka gabata mamaki.

'Yan kungiyar taliban a Afghanistan
'Yan kungiyar taliban a Afghanistan - AFP

'Yan Taliban sun kama Ismail Khan daya daga cikin manyan kwamandojin dake yakar su a yankin. Heralt.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.