Isa ga babban shafi
RIKICIN-AFGHANISTAN

Ba zamu bar Afghanistan ta zama dandalin ayyukan ta'addanci ba - Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yace ba zasu bari Afghanistan ta sake zama dandalin ayyukan ta’addanci ba kamar yadda take kafin Amurka ta jagorancin mamaye ta shekaru 20 da suka gabata.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron © TFI / Screenshot de la diffusion internet
Talla

Yayin da yake jawabi ga jama’ar kasar sa, Macron ya bayyana cewar za suyi iya bakin kokarin su tare da Rasha da Amurka da kuma sauran kasashen Turai wajen aiwatar da manufar su ta tsaro da zaman lafiya bayan kungiyar Taliban ta kwace iko a kasar.

Shugaban ya bayyana halin da ake ciki a Afghanistan a matsayin mai matukar muhimmanci ga tsaron su da kuma yaki da abokan gabar su ta bangaren ta’addanci.

Shugabannin Taliban a fadar shugaban kasa
Shugabannin Taliban a fadar shugaban kasa - AL JAZEERA/AFP

Macron yace babban abinda ke gaban su shine yaki da tsatsauran ra’ayi ta kowacce fanni, yayin da ya bayyana cewar kungiyar Turai zata gabatar da wani shiri domin tinkarar matsalar ‘yan gudun hijirar dake barin kasar da kuma dirar mikiya akan masu safarar mutanen da za’a samu.

Shugaban yace Faransa da Jamus da wasu kasashen Turai zasu mayar da martani mai karfi na hadin gwuiwa domin dakile safarar baki ta barauniyar hanya kamar yadda dokokin turai suka tanada.

Macron yace ya zama wajibi su shirya kare kan su ta hanyar kwararar baki ta barauniyar hanyar da zai jefa rayuwar su cikin hadari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.