Yan Taliban sun kwace mulkin Afghanistan
Kungiyar Turai da sauran kasashe na Yammacin Duniya, sun ce yanzu haka suna daukar matakai don kare lafiyar jami’ansu da ke rayuwa a kasar ta Aghanistan, musamman a daidai wannan lokaci da mayakan Taliban suka kwace mulkin kasar.
Wallafawa ranar:
Ashraf Gani tsohon Shugaban kasar da ya gudu ,ya ce ya bar kasar ne don kaucewa zubar da jinin fararren hula,yayinda yan Taliban suka kama fadar Shugaban kasar,suna kuma dakon isowar jagororin su daga Qatar.
Tuni kasashen yamma ciki har da Canada, Jamus, Faransa, Amurka da kuma Birtania, suka tsara yadda za su kwashe jami’ansu na diflomasiyya daga kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu