Isa ga babban shafi
Amurka - Afghanistan

Amurka ta yi gargadin yiwuwar samun wani sabon hari a Kabul

Amurka ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar sake kai wani harin ta’addanci makamancin wanda aka kai  a filin jirgin  saman Kabul nan da ‘yan sa’o’i.

Kabul's international airport
Kabul's international airport AFP
Talla

Bayan da ya samu bayanai daga tawagarsa ta tsaron kasa, shugaba Joe Biden ya fada a wata sanarwa cewa za a ci gaba da kai harin jirgi mara matuki a kan kungiyar Khorasan ta IS da ta dauki alhakin mummunan harin Kabul.

Biden ya ce yanayin da ake ciki a halin yanzu yana da matukar hadari, kuma har yanzu akwai barazanar hare haren ta’addanci a filin tashi da saukar jiragen sama na Kabul, yana mai cewa kwamandojinsa sun shaida masa yiwuwar hakan.

Fiyeda mutane dubu 112 ne suka tsere daga Afghanistan ta wurin shirin kwashe mutane dac Amurka ke jagoranta tun da Taliban ta kwace mulkin kasar makonni 2 da suka wuce.

Fiye da mutane 100 suka mutu a harin da IS ta kai yayin kwashe mutane a filin jirgin saman Kabul, ciki har da dakarun Amurka 13.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.