Isa ga babban shafi
Amurka - Afghanistan

Dakarun Amurka 12 sun mutu, 15 sun jikkata a harin Kabul

Dakarun Amurka 12 ne suka mutu, kana 15 suka jikkata a wasu tagwayen fashe fashe a wajen filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Kabul, sa’oi bayan da kasashen yammacin duniya suka yi gargadin yiwuwar kai harin ta’addanci a inda dubban mutane ke kokarin ficewa daga kasar, hare haren da kungiyar IS mai ikirarin jihadi ta dauki alhakin kaiwa.

Kwmandan sojin Amurka Janar Kenneth Mckenzie.
Kwmandan sojin Amurka Janar Kenneth Mckenzie. REUTERS - STAFF
Talla

Sai gawargwakin mutane ake gane baje a wata magudanar ruwa mara zurfi dake inda fashe fashen suka auku, a yayin da masu aikin ceto ke kwasar wadanda suka jikkata male-male cikin jini don nema musu magani.

Jagoran rundunar tsaron Amurka, Janar Kenneth Mckenzie, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya  ce abubuwan da ake zato bam ne sun fashe a tsakiyar dimbim jama’ar da ke fatan darewa jiragen saman da ke kwasar mutanen da suke gujewa mulkin ‘yan Taliban

Shugaban Amurka John Biden ya bayyana fargabar samun irin wannan harin daga ‘yan ta’addan ISIS sakamakon yawan mutanen da ake da su a tashar jiragen dake kokarin ficewa daga kasar.

Kungiyar Taliban da ma sauran kasashen duniya sun yi Allah wadai da wadannan hare hare, inda ministan harkokin wajen Italiya Luigi Di Maio ke caccakar tir da lamarin, a yayin da kasarsa ke ci gaba da kwashe wasu ‘yan Afghanistan da ke neman barin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.