Faransa da India sun kulla sabon kawance don aiki tare a Pacific
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da takwaransa Firaministan India Narendra Modi sun cimma jituwa kan kudirin aiki tare a yankin Pacific, sabuwar alakar da ke kulluwa bayan takaddamar kwangilar jirgin ruwan yakin karkashin teku tsakanin Faransar da Australia.
Wallafawa ranar:
Matakin kulla kawancen na India da Faransa zai baiwa kasashen biyu damar aiki tare a yankin na Pacific da ya fi kusanci da Australia wadda yanzu ta zama abokiyar fadar Faransa.
A zantawarsu ta wayar tarho yau talata, shugabannin biyu sun amince sun karfafa alakarsu ta fuskar kere-kere da kimiyya da kuma tsaro baya ga kasuwanci.
Yayin zantawar ta su Macron ya roki Narendra Modi kan rike amanar juna don kaucewa matsalar da Faransar ta samu a baya-bayan nan da Australia.
Emmanuel Macron ya sha alwashin kyautata sabon kwancen tsakanin kasar ta Turai da India daga gabashin Asiya a wani yunkuri na karfafa kasancewarsu a yankin na Pacific da manyan kasashe ke ci gaba da girke jirage da makamai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu