Isa ga babban shafi
Algeria - Faransa

Macron ya nemi gafara kan yadda Faransa ta wulakanta mayakan Harkis

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya nemi afuwar wasu 'yan Algeria a madadin kasar sa, wadanda aka yi watsi da su, bayan da suka taimakawa Faransa wajen yakar masu neman ‘yancin kan kasar ta su da ke arewacin Afirka.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. © REUTERS/ Guillaume Horcajuelo/Pool
Talla

Fiye da 'yan Algeria dubu 200 ne suka taimakawa sojojin mulkin mallaka na Faransa a yakin da suka gwabza da mayaka masu neman ‘yanci kasar ta Algeria daga shekarar 1954 zuwa 1962.

Bayan Karkare yakin da bangarorin biyu suka fafata da ya kunshi cin zarafi gami da azabtar da dubban mutane ne, gwamnatin Faransa a waccan lokacin ta yi watsi da mayakan sa kan da suka yi mata biyayya da aka fi sani da Harkis duk da alkawuran da tayi a baya cewa za ta kula da su, matakin da ya jefa su cikin kunci.

Wasu mayakan sa kai na Algeria da aka fi sani da Harkis, wadanda suka taimakawa Faransa wajen yakar masu neman 'yan cin kai.
Wasu mayakan sa kai na Algeria da aka fi sani da Harkis, wadanda suka taimakawa Faransa wajen yakar masu neman 'yan cin kai. © Jacques GREVIN INTERCONTINENTALE/AFP/File

Kididdiga ta nuna cewar bayan karewar yakin neman ‘yan cin kan Algerian a ranar 18 ga watan Maris na 1962, mayakan Harkis dubu 42 ne kawai hukumomin Paris suka baiwa damar komawa Faransa wasunsu tare da iyalansu, yayin da kuma aka bar kimanin mayakan sa kan dubu 90 a Algeria, matakin da ya baiwa sabbin shugabannin kasar damar yiwa akasarinsu kisan kiyashi, a matsayin daukar fansar cin amanar kasar su da suka yi.

A shekarar 2001, masu fafutukar kare hakkin dan adam da suka yi yunkurin ganin an hukunta gwamnatin Algeria kan laifukan yakin da ta aikata, sun yi ikirarin cewa mayakan na Harkis dubu 150, shugabannin waccan lokaci suka kashe a kasar ta Algeria, a matsayin fansar taimakawa Faransa.

Bincike dai ya nuna a halin yanzu, iyalan mayakan sa kan da suka taimakawa Faransa yayin yakin neman ‘yancin Algeria akalla dubu 400 ke zaune a sassan kasar da ta yiwa kakkaninsu mulkin mallaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.