Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya amince Faransa ce ta kashe Boumendjel

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a karon farko ya amince cewar sojojin kasar ne suka azabtar da jagoran neman ‘yancin kan Algeria Ali Boumendjel kana suka yi rufa-rufan kisan sa da aka yi.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS - POOL
Talla

Yayin ganawa da jikokin Boumendjel guda 4, Macron ya amsa cewar tabbas an tsare mahaifinsu, aka azabtar da shi kana aka kashe shi a ranar 23 ga watan Maris na shekarar 1957.

Kafin yanzu, hukumomin Faransa sun bayyana cewar Boumendjel ya kashe kansa ne lokacin da ake tsare da shi, abin da iyalinsa ta yi ta fafutukar ganin an sauya shi har zuwa lokacin da ya mutu a watan Agustan bara.

Fadar Macron ta ce amincewa da abin da ya faru a baya da kuma fadin gaskiya ba zai warkar da raunin da aka samu ba, amma kuma zai bude kofar hangen gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.