Isa ga babban shafi
Faransa-Algeria

Faransa ba za ta nemi ahuwar Algeria ba kan barnar da ta tafka - Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yace kasar ba za ta nemi afuwa kan barnar da ta tafka a Algeria ba, ciki har da yiwa ‘yan kasar kimanin miliyan 1 da rabi kisan gilla, a tsawon shekaru 132 da ta shafe tana yi mata mulkin mallaka.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Sanarwar da ofishin shugaba Macron ya fitar tace Faransa ba za ta taba neman afuwa ko biyan diyyar laifukan da ta aikatawa Algeria ba, a tsawon shekaru 8 da suka shafe suna gwabza yakin da yakwo karshen mulkin mallakar da Faransa tayi mata, sai dai za ta dauki dukkanin matakan da suka dace wajen kyautata alakarta da kasar ta Algeria.

Har yanzu dai babu wata kwakkwarar dangantaka tsakanin Faransa da Algeria, saboda laifukan yakin da auka aikatawa juna a tsawon lokacin da suka shafe suna gwabza fada neman ‘yanci daga shekarar 1954 zuwa 1962, kimanin shekaru 60 da suka gabata.

Wani lokaci a yau Laraba kwamitin da shugaba Emmanuel Macron ya kafa kan nazartar yakin na Algeria da kuma gyara alakarsu zai gabatar da rahotonsa.

A shekarun 1930 ne Faransa ta mamaye Algeria, a lokacin da take karkashin daular Musulunci ta Ottoman.

A shekarar 1954 kuma kungiyar ‘yan tawayen FLN ta kaddamar da yakin neman kwatar ‘yanci, wanda a yayin yakin ne dakarun Faransa suka yiwa ‘yan Algeria tsakanin dubu 6 zuwa dubu 30 kisan gilla a birnin Setif da kuma yankin Constantine dake yankin arewa maso gabashin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.