Isa ga babban shafi

Faransa za ta sake salon yaki a Sahel - Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce gwamnatinsa za ta sake fasalin yaki da ‘yan ta'adda a yankin Sahel, sakamakon nasarorin da rundunar Barkhane ta samu, da kuma kokarin kawayensu na kasashen Turai.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron,
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, (Ludovic Marin / POOL via AP)
Talla

Yayin da ya ke aikewa da sakon fatan alheri ga sojojin kasar a barikin Brest, Macron ya ce nasarorin da dakarun Faransa suka samu a Sahel da kuma rawar da dakarun kasashen Turai suka taka, zai ba su damar sake fasali a yankin dake dauke da sojojin kasar 5,100.

Wannan wani tabbaci ne dangane da shirin gwamnatin kasar na rage yawan sojojin ta dake yankin wadanda ke yaki da ‘yan ta’adda tun daga shekarar 2013.

A taron da Macron yayi da takwarorin sa na kasashen Mauritania da Mali da Burkina Faso da Nijar da kuma Chadi, a watan Janairun shekarar 2020,  ya jaddada muhimmacin yaki da ‘yan ta’adda da kuma kara yawan sojoji 600 domin fuskantar matsalar da ake samu.

Ana sa ran Faransa ta bayyana shirin rage yawan dakarun ta a taron kungiyar G5 Sahel da zai gudana a watan gobe a birnin N’Djamena.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.