Isa ga babban shafi
Faransa-Algeria

Macron ya bada damar isa ga bayanan sirri a kan yakin Algeria

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya bayar da damar isa ga bayanan sirrin kasar na tsawon shekaru 50, musamman ma wadanda suka shafi yakin neman ‘yancin-kai da ‘yan gwagwarmayar Algeria suka gwabza da dakarun kasar ta Faransa.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. Ludovic MARIN AFP
Talla

Batun bayar da damar isa ga bayanan sirrin, na daga cikin shawarwarin da kwamitin da gwamnatin Faransa ta kafa karkashin jagorancin wani malamin tarihi mai suna Benjamin Stora ya bayar, domin samar da haske a game da laifufukan da ake zargin sojojin Faransa da aikatawa lokacin wannan yaki.

Fadar shugaba Macron, ta ce daga ranar laraba ta wannan mako, za a bayar da damar isa ga bayanan sirri na ma’aikatar tsaron kasar, wanda hakan zai bai wa masu zargin Faransa da aikata ba daidai ba, damar isa ga wasu muhimman bayanai a lokacin wannan yaki na neman ‘yanci.

Wannan mataki dai na zuwa ne mako daya, bayan da shugaba Emmanuel Macron ya amince ‘’a madadin  Faransa’’, cewa lauya, kuma shahararren dan kishin kasar Algeria Ali Boumendjel, sojin Faransa sun gallaza masa azaba ne har sai da ya mutu a 1957 daidai lokacin da ake gwabza wannan yaki.

A ranar 20 ga watan janairun da ya gabata ne malamin tarihi Benjamin Stora, ya gabatar wa mahukuntan Faransa sakamakon binciken da ya gudanar dangane da abubuwan da suka faru a wannan yaki da ya sa auku sakamakon yadda ‘yan Algeria suka dauki makamai

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.