Za’a dawo da hukuncin yanke hannu a Afghanistan
Kungiyar Taliban, ta bayyana cewa, za’a dawo da zartas da yanke hukuncin yanke hannu, da na kisa ga wanda suka aikata laifin da ya kai a yanke musu hukuncin a Afghanistan.
Wallafawa ranar:
Shugaban hukumar gidajen yari na kungiyar Taliban, Mullah Nooruddin Turabi, ya shaidawa manema labarai cewa, wannan hukunci ya zama wajibi don tabbatar da tsaro.
Ya ce, ba za’a dinga aiwatar da shi a bainar jama’a ba, ba kamar yadda ya gudana a tsohon mulkin Taliban a cikin shekarar alif 990 ba.
Tin lokacin da Taliban ta kwace mulkin a 15 ga watan Agustan shekarar da muke ciki ne ta yi alkawarin gudanar da mulki, ba tsangwama, ba kamar yadda suka yi a tsohon mulkin su ba.
Amma a halin yanzu, ana ta samun rahotannin da suka shafi tauye hakkin bil’adaman da ‘yan kungiyar ke yi a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu