Isa ga babban shafi
ANNOBAR-KORONA

Hukumar Lafiya tace korona ta kashe ma'aikatan lafiya tsakanin dubu 80 zuwa 180

Hukumar Lafiya ta Duniya tace akalla ma’aikatan lafiya tsakanin dubu 80 zuwa dubu 180 suka mutu sakamakon harbuwa da cutar korona daga watan Janairun bara zuwa watan Mayun bana.

Shugaban Hukumar Lafiya Tedros Adhanom Gebreyesus
Shugaban Hukumar Lafiya Tedros Adhanom Gebreyesus AP - Martial Trezzini
Talla

Shugaban Hukumar Tedros Adhanom Gebreyesus ya bayyana cewar saboda muhimmancin aikin da jami’an kula da lafiya keyi, ya dace a saka su a sahun gaba wajen mutanen da za’a baiwa allurar rigakafin, yayin da ya sake sukar matsalar da ake samu wajen fifita wasu kasashe dangane da shirin yin allurar rigakafin.

Hukumar tace alkaluman da aka samu daga kasashe 119 na nuna cewar an yiwa ko wadanne ma’aikatan lafiya 2 daga cikin 5 rigakafi, yayin da adadin ya sha banban tsakanin shiya zuwa shiya.

Maganin rigakafi samfurin Sinopharm
Maganin rigakafi samfurin Sinopharm Munir Uz zaman AFP/File

Gebreyesus yace a nahiyar Afirka, kasa da mutum guda daga cikin ma’aikatan lafiya 10 suka karbi rigakafin, yayin da a kasashen da suka ci gaba an yiwa sama da kashi 80 na ma’aikatar lafiyar rigakafin har sau biyu.

Shugaban Hukumar yayi kira ga kasashen duniya da su tabbatar da cewar sun baiwa jami’an kula da lafiyar kasashen su muhimmanci wajen bada maganin rigakafin annobar koronar saboda illar da suke fuskanta wajen gudanar da ayyukan su.

Tedros yace watanni 10 bayan kaddamar da maganin rigakafin cutar da Hukumar ta amince da shi, har yanzu miliyoyin jami’an kiwon lafiya basu karbi allurar ba, kuma wannan abin kunya ne ga kasashen da suke da kuma kamfanonin dake samar da magungunar.

Jami'an kula da lafiya
Jami'an kula da lafiya AFP - JODY AMIET

Annette Kennedy, shugabar kungiyar masu taimakawa likiti ta duniya, tace kungiyar tasu na bayyana bakin cikin ta dangane kowanne jami’in kiwon lafiyar da ya rasa ran sa, wadanda suka hada da ganganci a wasu lokuta.

Jami’ar ta bayyana cewar abin kunya ne akan gwamnatocin kasashen da suka gaza wajen kare lafiyar ma’akatan su, abinda ya kaiga rasa rayukan su.

Hukumar Lafiya na bukatar ganin kowacce kasa ta yiwa akalla kashi 40 na mutanen ta allurar rigakafin nan da karshen wannan shekara, yayin da Tedros ke cewa kasashe 82 na fuskantar barazanar gazawa wajen cimma wannan adadi saboda rashin samun isasshen maganin rigakafin.

Annobar korona ta kashe mutane miliyan 4 da dubu 900 tun bayan barkewar ta a watan Disambar shekarar 2019, yayin da cutar ta kama mutane kusan miliyan 242 a fadin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.