Isa ga babban shafi
Rasha - Coronavirus

An maido da dokar takaita zirga zirga a Moscow saboda karuwar korona

Hukumomin Birnin Moscow dake kasar Rasha sun sanya dokar takaita zirga zirga sakamakon karuwar masu kamuwa da cutar korona, bayan samun mutane 1,015 da suka mutu a rana guda.

Yadda ake feshin maganin saboda karuwar masu kamuwa da cutar korona a Rasha 19/10/21.
Yadda ake feshin maganin saboda karuwar masu kamuwa da cutar korona a Rasha 19/10/21. REUTERS - MAXIM SHEMETOV
Talla

Magajin Garin birnin Sergei Sobyanin ya bukaci masu sama da shekaru 60 da basu karbi allurar rigakafi ba da su zauna a gidajen su, yayin da aka bukaci daukacin ma’aikata kuma su kai kan su domin karbar allurer.

Sobyanin ya kuma baiwa kamfanonin umurnin tura ma’aikatan su kasha 30 domin gudanar da ayyukan su daga gida.

Ya zuwa wannan lokaci mutane 225,325 suka mutu sakamakon harbuwa da cutar a Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.