Isa ga babban shafi
India-WHO

WHO ta sahale fara amfani da rigakafin corona na Covaxin da India ta samar

Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta sahale fara amfani da nau’in rigakafin corona na Covaxin da kamfanin Bharat Biotech na India ya samar bayan gwajinsa tare da gano tasirinsa a yaki da cutar wadda zuwa yanzu ta hallaka mutane fiye da miliyan 5 a sassan Duniya.

Tuni India ta fara yiwa jama'arta allurar rigakafin na Covaxin.
Tuni India ta fara yiwa jama'arta allurar rigakafin na Covaxin. Prakash Singh AFP/Archivos
Talla

Hukumar ta WHO ta ce za a iya fara amfani da nau’in rigakafin na Covaxin samfurin India a yanayi na gaggawa don yaki da cutar ta covid-19 da ke ci gaba da kisa a sassan Duniya.

Nau’in rigakafin na Covaxin shi ne irinsa na farko da aka samar tare da yin gwajinsa cikin kasar India kuma WHO ta sahale amfani da shi inbanda sauran rigakafi da kamfanonin magani na kasar ke taya aikin samar da su.

Acewar hukumar ta WHO nau’in rigakafin na da sahihancin kashi 78 wajen yaki da cutar ta covid-19 bayan gwajin allurarsa sau bibbiyu kan jama’a cikin makwanni 4 da suka gabata.

WHO ta bayyana cewa nau’in rigakafin na Covaxin zai yi tasiri hatta a kanana da matsakaitan kasashe la’akari da saukinsa wajen adanawa da kuma dadewar da ya ke gabanin lalacewa.  

Nau’in rigakafin na India ya zama rigakafi na 8 da zuwa yanzu Duniya ke amfani da shi don yakar cutar bayan Pfizer da BioNTech da Moderna da AstraZeneca da Johnson and Johnson baya ga Sinopharm da Sinovac.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.