India za ta samar da alluran rigakafin Covid da dama zuwa kasashen Duniya
Kasar India a jiya asabar ta bakin wani jami’in kiwon lafiyar kasar,mai cewa kasar kam ta shirya yanzu na ganin ta fitar da kusan alluran rigakafi da cutar Covid 19 milyan takwas nan da karshen watan Oktoba mai kamawa.
Wallafawa ranar:
Wannan dai na daga cikin alkawuran da Firaministan kasar Narendra Modi ya yi a wani taro da ya hada kasashen Amurka,Japan da Australia a birni Washington ranar juma’a da ta gabata.
Wadanan allurai za su isa yankunan Asiya da Pacifik,yankunan dake ta kokarin ganin sun kare al’umar su daga kamuwa da wannan cuta.
Alluran na Johnson&Johnson za samar da su a India a karkashin izinin wani kamfanin kasar ta Indiya mai suna Biological-E a cewar Ministan harakokin wajen Indiya Harsh Vardhan Shringla,wanda a karshe ya ce yin haka daga India tareda goyan bayan Amurka zai rage kafin China a wannan tafiya na yaki da wannan cuta a wadanan yankuna.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu