Isa ga babban shafi

Ya kamata Ronaldo da Messi suyi ritaya (Michel Platini)

Tsohon Shugaban hukumar kwallon kafar Turai ,Michel Platini a wata hira da jaridar La Gazetta Dello Sport, tsohon tauraron kungiyar Juventus  Turin na kasar Italiya ya na mai nazari kan makomar taurarun  tamola da suka hada  Christiano Ronaldo da Lionnel Messi.

Lionel Messi dan wasan Barcelona da Cristiano Ronaldo lokacin da alkalin wasa ke nuna yalon kati ga Ronaldo a Wasan Classico tsakanin Real Madrid da Barcelona
Lionel Messi dan wasan Barcelona da Cristiano Ronaldo lokacin da alkalin wasa ke nuna yalon kati ga Ronaldo a Wasan Classico tsakanin Real Madrid da Barcelona Reuters
Talla

Michel Platini ya na mai kallon wadanan yan wasa Christiano Ronaldo mai shekaru 37 da Lionnel Messi mai shekaru 34 a matsayin yan wasan da suka kafa tarihi a duniyar tamola,sai dai a cewar sa sanun a hankali sun kama hanyar bankwana da kwallon kafa a hukumance.

Michel Platini,Tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Turai ta UEFA
Michel Platini,Tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Turai ta UEFA REUTERS/Ruben Sprich

Dalili a cewar sa,Christiano da Messi,Duniya ta sheida cewa  taurarun ne,kuma kowane daga bangaren say a taka muhimiyar rawa da kungiya da suka fi share dogon lokaci.

Platini ya bayyana cewa daya daga cikin kuskuren da yan wasan suka yi ,a kakar shekara ta 2021 su canza kungiya, Christiano ya koma da kungiyar Manchester United,yayinda Lionnel Messi ya koma da kungiyar  PSG.

Lionel Messi da Cristiano Ronaldo
Lionel Messi da Cristiano Ronaldo AFP/Archives

Wanna zabi a cewar Michel Platini ya sa shi dogon nazari,inda tsohon tauraron kungiyar kwallon kafar Faransa  y ace shi kam ,ya dau niyar ritaya daga duniyar tamola  ya na mai shekaru 32, a wancan lokaci ya na da zabi,hau ya ci gaba da taka leda da kungiyoyi irin su Barcalona,ko kungiyar Marseille,sai dai a maimakon ya yi haka ,ya komaci shiga tarihi da kafar dama ,musaman indan aka tuna da shi a tuna da kungiyar da ya kafa tarihi ya kuma rataye takalman sa a kai. A karshe Michel Platini ya bayyana cewa indan aka yi maganar Ronaldo sanin kowa ne  Real Madrid ce,yayinda Lionnel Messi  Barcalona.

har indan suna suke nema yanzu kam,ganin ta yada matasa ke yunkurowa, shi a zabin sa zai nemi zuwa Amurika ko China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.