Isa ga babban shafi

Dala milyan 500 a matsayin tallafi don kare fararen hula a zagayen Tafkin Chadi

Majalisar Dinkin Duniya tare da kungiyoyin agaji, sun sanar da tallafin kudaden da suka zarce dala miliyan 500 domin amfani da su wajen kare fararen hular dake fuskantar barazana daga ‘yan ta’addan da ke ci gaba da kai munanan hare hare a yankin. 

Al'ummomin da ke rayuwa cikin yanayin kunci a zagayen Tafkin Chadi,22 ga watan oktoban 2022.
Al'ummomin da ke rayuwa cikin yanayin kunci a zagayen Tafkin Chadi,22 ga watan oktoban 2022. REUTERS - CHRISTOPHE VAN DER PERRE
Talla

Bayan wani taro da suka gudanar a Jamhuriyar Nijar, kasashen duniya tare da masu bada agaji sun sanar da wadannan kudade domin karkata su wajen ayyukan jinkai da tsaro a kasashe 4 na zagayen Tafkin Chadi. 

Wakilan da suka halarci taron na Nijar sun mayar da hankali ne akan yadda za’a karfafa gwuiwar mutane sama da miliyan 24 da rikicin boko haram ya daidaita a kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi. 

A birnin Berlin dake kasar Jamus, masu bada agaji sun sanar da gudumawar sama da Dala biliyan 2 da miliyan 150 domin aikin jinkai da kuma tabbatar da zaman lafiya. 

Majalisar Dinkin Duniya tace kudaden da ake bukata wajen aikin jinkai a yankin ya karu da dala miliyan 259 tun daga shekarar 2018. 

Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar dake kula da jinkai Joyce Msuya tace muddin ba’a shawo kan matsalolin dake haifar da rikicin ba, ba za’a taba warkar da ciwon da ya haifar ba. 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.