Afrika ta Kudu na fama da matsalar rashin daidaito
Wani rahoto da bankin duniya ya fitar ya bayyana Afrika ta Kudu a matsayin kasar da ta fi fama da matsalar rashin daidaito a duniya, kuma wariyar launi na daya daga cikin matsalolli da suka jibanci rashin daidaito tsakanin al’umma.
Wallafawa ranar:
Rahoton ya ce, kashi 10 na al’ummar Afrika ta kudu sun mallaki sama da kashi 80 na dukiyar kasar.
Duk da cewa, kimanin shekaru 30 kenan da aka kawo karshen mulkin wariyar launin fata a Afrika ta Kudu, amma har yanzu kasar na fama da matsalar ta nuna wariya, abin da ake kallo a matsayin na kan gaba wajen ta’azzara rashin daidaiton.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu